Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Muka Kashe Dan Sanata Bala Na'Allah


Marigayi Kyaftin AbdulKarim Na'Allah
Marigayi Kyaftin AbdulKarim Na'Allah

Wadanda ake zargi da kisan dan Sanata Bala Na’Allah sun shiga hannu, sun kuma bayyana dalili da kuma yadda suka kashe Abdulkarim Bala Na’Allah.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta gabatar da wasu matasa biyu, Bashir Muhammad mai shekaru 23, da Nasiru Balarabe mai shekaru 27, da ake tuhuma da kisan dan Sanata Bala Na’Allah, Captain Abdulkarim Na’Allah makwanni biyu da suka gabata.

A yayin da suke karba tambayoyin manema labarai, daya daga wadanda ake zargin, Nasiru Balarabe, ya ce su uku ne suka gudanar da danyen aikin da yayi sanadiyyar mutuwar Abdulkarim, su biyu tare da na ukunsu Usman Dankano, wanda ba’a sami kamawa ba ya zuwa yanzu.

Shi kuwa Bashir Muhammad cewa yayi bai taba sanin marigayin ba kafin su kai farmaki a gidansa.

“Wata rana ne muna tafiya ni da Dankano muka bi ta kofar gidansa, sai muka ga mota a ajiye a cikin harabar gidan, kawai sai Dankano ya ce za mu zo mu sace motar,” in ji Muhammad.

“Washe gari sai aka tashi da ruwan sama, saboda haka sai muka yanke shawarar zuwa gidan. Bayan mun shiga, ni da Nasiru muka bude kofa Dankano ya shigo rike da fitilar hannu.”

“Hasken fitilar ne ya janyo hankalin mai gidan har ya gan mu, nan take ya dauko wani abu a karkashin gado ya tunkaro mu, inda ya soma kokawa da Balarabe.”

“A lokacin kokawar ne sai marigayin ya fadi, mu kuma muka yi amfani da igiyar shanya tufafi muka daure shi, daga nan bai sake magana ba, sai muka dauki makullin motar muka fice.”

Wadanda ake zargin sun ce sun sayar da motar ne a Katsina kan kudi naira miliyan daya.

To sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Kaduna ASP Muhammad Jalige, ya ce an kiyasta motar tana kudi naira miliyan 9.

Jalige ya bayyana cewa wadanda ake tuhumar sun sayar da motar ne a Jamhuriyar Nijar, kuma tuni da ‘yan sanda suka gano ta, inda ya ce suna hadin gwiwa da ‘yan sandan kasa-da-kasa domin dawo da ita.

Idan za’a tuna, a ranar 26 ga watan Agusta ne aka sami gawar babban dan na Sanata Bala Na’Allah a gidansa da ke unguwar Malali GRA a garin Kaduna.

Marigayi Abdulkarim Na’Allah dai matukin jirgin sama ne, kuma ya rasu yana da shekara 36 a duniya.

XS
SM
MD
LG