Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya tsalleke rijiya da baya, a lokacin da wasu ‘yan Najeriya mazauna kasar Spain suka far masa.
Amaechi ya bayyana hakan ne a shafinsa an Twitter a yau Juma'a.
Ministan na wakiltar Najeriya ne, a taron da ke gudana a birnin Madrid na kasar Andalus.
“Wasu tsirarun ‘yan Najeriya da ba su san me ke faruwa ba, sun far min, yayin da nake wakiltar kasa ta a taron sauyin yanayi a Madrid na kasar Spain.”
Ya kara da cewa, amma “kafin a yi min illa, ‘yan sandan Spain sun yi maza sun shiga tsakani. Kuma babu abin da ya same ni. Na gode da goyon bayanku da addu’o’inku.”
Wannan dai ba shi ne karon farko da ‘yan Najeriya mazauna wasu kasashen waje ke kai hari kan manyan jami’an gwamnati ba.
Ko a ‘yan watannin baya, wasu da ake zargin masu fafutukar kafa kasar Biafra, sun far wa tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu a kasar Jamus.
Za ku iya son wannan ma
-
Mayu 27, 2023
Na Zaku In Mika Mulki – Buhari