Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Porto Ta Sallami Juventus a UEFA


Dan wasan Juventus Cristiano Ronaldo, yana takaicin ficewa daga gasar UEFA

Porto ta kai ga zagayen kusa da na karshe a gasar cin kofin zakarun Turai TA UEFA bayan da ta kada Juventus a wasan da suka kara.

Dan wasan Porto Sergio Oliveira ya kai kungiyar zagayen kusa da na karshe a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai, bayan da ya zura kwallo a zangon karin lokacin da aka yi.

Juventus ta lashe wasan da ci 3-2, amma duk da haka an fitar da ita daga gasar saboda jimullar kwallayen wasannin biyu da kungiyoyin biyu suka buga ya tashi a 4-4.

Porto dai ta buga wasan ne da ‘yan wasa 10 bayan da aka kori Mehdi Taremi, amma nasarar samun kwallayen da suka yi a waje, ta kai su ga gaci.

Shi dai dan wasan Oliveira, shi ya zura kwallon farko ga Porto daga inda ake buga fenarti.

Amma dan wasan Juventus, Federico Chiesa ya ci wa Juve kwallaye biyu bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

Hakan ya kai wasan ga kunnen doki, har aka tashi kuma babu wanda ya kara kwallo, abin da ya sa aka kara lokaci.

A dai ranar 19 ga watan Maris za a fitar jerin kungiyoyin da za su kara a zagayen na kusa da na karshe ko kuma semi-finals a gasar ta Champions League.

Wannan shi ne karo na biyu da Juventus take ficewa daga gasar a jere a wannan zagayen.

AFCON 2021, Troost-Ekong

Abin da kyaftin Troost-Ekong ya ce da Najeriya ta lashe wasanninta uku a jere bayan doke Guinea-Bissau
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:15 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021, Super Eagles

Yan wasan Najeriya na atisaye gabanin karawar da za su yi da Guinea-Bissau a rukunkin D na gasar AFCON
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:08 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021: Troost-Ekong

Kowa ya san cewa mun iya taka leda’ In ji Troost-Ekong, yayin da Najeriya ta kai zagayen knockouts
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:03 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021, Kelechi Iheanacho

"Ku doke daya daga cikin shahararrun koci a duniya", Kelechi Iheanacho, Najeriya bayan sun doke Masar
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:11 0:00
Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG