Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Wani Hari Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutum 23 a Sokoto


Wasu ‘yan bindiga sun kai wani hari a jihar Sokoto wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 23, tare da raunata wasu 13 sakamakon harbe-harben bindiga.

Rundunar 'yan sandan jihar ta Sokoto ta tabbatar da faruwar lamarin wanda ya auku a garin Sabon Birni da ke jihar.

Ta kuma bayyana cewa ya zuwa yanzu wadanda suka samu raunuka suna jinya a asibiti.

Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Muhammad Abubakar Sadiq, ya sheda wa Muryar Amurka yadda yankin gabashin Sokoto ke yawan fuskantar barazana.

Ya ce “muna tsaye dare da rana domin kawo karshen wannan matsalar da muke fuskanta, domin kare lafiyar mutanenmu da kuma dukiyoyinsu.”

Da ma dai ana yawan kai hare-hare a jihar ta Sokoto, lamarin da ya jefa mutanen jihar cikin zullumi da fargaba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG