Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Zaben Jihar Edo Ya Kaya


Wata rumfar zabe a Abuja babban birnin Najeriya.
Wata rumfar zabe a Abuja babban birnin Najeriya.

Al’umar jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya sun dunguma zuwa rumfanan zabe a ranar Asabar domin zabo wanda zai shugabancin jihar har na tsawon shekara hudu.

Rahotanni sun nuna cewa da sanyin safiyar ranar ta Asabar masu kada kuri’ar suka garzaya rumfunan zaben domin sauke nauyin da ya rataya a wuyansu, inda a wasu mazabu aka yi ta korafin rashin zuwan kayan aiki akan kari, yayin da a wasu kuma aka samu akasin hakan.

Manyan ‘yan takara a zaben sun hada da gwamna mai ci Godwin Obaseki mai shekara 63, wanda ya sauya sheka ya koma PDP daga APC.

Sai dan takara Osagie Ize-Iyamu mai shekara 58 wanda jam’iyyar adawa ta APC a jihar ta tsayar.

Shi dai Obaseki na neman wa’adi na biyu ne domin a shekarar 2016 ya lashe zabe karkashin jam’iyyar APC.

Bayanai sun yi nuni da cewa, gwamna Obaseki da abokin hamayyarsa Ize-Iyamu duk sun ci mazabunsu a cedar sakamakon farkon da ya fito.

Akalla 'yan takara 14 ne suka neman kujerar gwamnan a jihar ta Edo mai kananan hukumomi 18.

Wannan zabe tamkar zakarin gwajin dafi ne ga manyan jam’iyyun biyu inda za su auna farin jininsu a wurin masu kada kuri’a.

Wakilin Muryar Amurka ya bayyana cewa akwai wasu wuraren da aka dan samu ‘yar hatsaniya kamar yadda wasu masu sa ido a zaben suka tabbatar masa.

“A can Unit 24-5 ne aka fara hayaniya saboda sun ga ba za su ci galaba ba sai aka fara rikici.” In ji wani mai sa ido kan zaben mai suna Yahaya Muhammed.

Sai dai ya ce daga baya an sasanta rikicin.

Wani abu da wakilin Muryar Amurka ya lura da shi shi ne, an yi ta take ka'idojin kiyaye yada cutar coronavirus inda wasu suka fita babu makarin baki da hanci.

Baya ga matsalar rashin isar kayayyakin zabe a wasu rumfuna akan kari, rahotanni sun ce an kuma fuskanci tangardar na’urar tantance katin zabe.

Bangaren jam’iyya mai mulki ta PDP ya yi ta korafi kan yadda aka samu wannan matsalar.

A baya dai hukumar zabe ta bayyana cewa, ta shirya tsaf domin gudanar da wannan zaben inda ta ce ta tanadi komai da komai.

A halin da ake ciki jama'a na can sun dakon sakamakon zaben.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG