Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yahudawa sun yi zanga-zanga akan jaririn Palasdinawa


Benjamin Netanyahu, Firaministan Isra'ila
Benjamin Netanyahu, Firaministan Isra'ila

Dubban Yahudawa sun yi zanga-zangar yin Allah wadai da harin ta’addancin da aka kaiwa wasu Palasdinawa da kona gidaje biyun da wani jariri dan watanni 18 da haihuwa ya kone kurmus.

Sannan an soki wasu masu jerin gwanon guda 6 da wuka, masu bin ‘yancin auren jinsi daya. Shugaba Reuven rivlin ya fadawa dandazon jama’a cewa tsana ta watsu a fadin kasar.

Sannan kuma bisa karya da gurbata addini da wasu ra’ayoyin bogi. Shugaban yace ana aikata ta’addanci da sunan Attaura littafin Yahuda.

Wasu Yahudawa da ake zargi ne suka kona wasu gidajen ‘yan Palasdinu a West Bank dake Dumaa a ranar juma’a.

Harin da har jariri dan watanni 18 da haihuwa ya babbake, iyayensa da dan uwansa kuma suna nan suna jinyar konewar da suka yi.

XS
SM
MD
LG