Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yajin Aikin Makarantun Kwalejin Kimiyya Da Fasaha: Rana Ta Hudu


Taron Manema Labaru na Kungiyar Malaman Kwalejoji
Taron Manema Labaru na Kungiyar Malaman Kwalejoji

Malaman makarantun kwalejin kimiyya da fasaha na Najeirya, sun ce ba za su dakatar da yajin aikinsu ba har sai an biya musu bukatun da suka nema.

Yajin aiki da kungiyar malaman makarantun kwalejin kimiyya da fasaha na Najeriya suka kaddamar domin yin gargadi ga hukumomin kasar yau ya shiga rana ta hudu.

Kungiyar ta ce babu wata barazana da za ta sa su janye daga yajin aikin.

Kungiyar mallam ta ce barazanar da ministan kwadagon Najeriya ya yi na cewa za a hana malaman albashi barzana ce kawai.

A wata hira da ya yi da Muryar Amurka, shugaban kungiyar malaman, Comrade Usman Yusuf Dutse, ya ce yanzu haka sanadiyar yajin aikin ana samun hadin kai tsakanin gwamnatin tarayya da ta jihohi, wadanda suka bukaci a dakatar da yajin aikin.

Usman ya kara da cewa ministan kwadago ya fito yana barazana a jaridu cewa yajin aikin da ake ba dai dai bane kuma zai dauki mataki akai.

Kungiyar malamai ta ce yin hakan ba zai gyara komai ba sai dai ya rikita al’mura.

A gefe guda kuma shugaban kungiyar dalibai a Kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Bauchi, Comrade Ibrahim Malam Danbam, ya roki dukkan bangarorin da su sasanta, kasancewar yajin aikin ya fi shafar dalibai.

Domin karin bayani saurari rahotan Abdulwahab Muhammad.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

XS
SM
MD
LG