Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yajin Aikin Masu A Daidaita Sahu Ya Saka Jama'a Cikin Tsaka Mai Wuya A Kano


Mashinan Keke-Napep (Facebook/PLSG)
Mashinan Keke-Napep (Facebook/PLSG)

A yayin da direbobin babura masu kafa uku da aka fi sani da a daidaita sahu suka shiga yajin aikin gamagari a yau Litinin a jihar Kano, dubban fasinjoji sun shiga tsaka mai wuya a kan tituna inda su ke takawa zuwa wuraren aiki da sauran hidimominsu.

Direbobin a daidaita sahun dai sun shiga yajin aikin ne don nuna bacin ransu game da matakin da hukumar kula da ababen hawa ta jihar da aka fi sani da KAROTA ta dauka na tilasta musu yin lasisin tuki a kan naira 18,000 da kuma sabuntawa a kan naira 8,500 don tuka baburan a jihar.

Rahotanni sun yi nuni da cewa karancin babura mai kafa biyu da kuma yajin aikin babura masu kafa uku wadanda sune kaso mafi yawa a bangaren hanyoyin sufurin jihar Kano ya tilastawa mutane da dama sun koma tafiya a kafa.

Lamarin dai ya sa wasu fasinjojin na amfani da kananan motocin daukar kaya wajen sufurin a halin yanzu, inda wasu kuma ke amfani da motocin bas-bas da na tasi da a baya aka rage amfani da su a cikin birnin na Kano sakamakon yadda baburan a daidaita sahu suka mamaye hanyar sufurin jihar kamar yadda wakilinmu a jihar ya tabbatar.

A nata bangare, hukumar KAROTA ta bayyana cewa ya zama wajibi direbobin su sabunta lasisin tukinsu a kan naira 8,500, sai kuma yi sabon lasisi a kan naira 18,000.

Dokar hukumar KAROTA dai ta fara aiki ne daga ranar daya ga watan Janairun shekara 2022 da muka shiga kamar yadda shugabanta, Baffa Babba Dan-Agundi ya tabbatarwa al’umman jihar Kano.

A wani bangare kuma, kungiyoyin direbobin baburan adaidaita sahu ta bayyana cewa a yarjejeniyar da suka cimma da KAROTA, babu batun sabunta lasisin a duk shekara, kamar yadda suka amince a baya.

Idan ana iya tunawa, a watan Fabrairun shekarar 2021 sai da direbobin na adaidaita sahu suka yi yajin aikin kwana uku saboda kakaba musu harajin naira 100 a kowacce rana da hukumar ta yi.

XS
SM
MD
LG