Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yakamata Al’umar Igbo Su Daina Kiran Biafra ! Cyril Okeke


Dangane da dambarwar dake gudana a Najeriya, wace ta hada da batun matasa ‘yan arewa dake cewa ‘yan kabilar Igbo, su bar arewacin Najeriya, ya jawo martani daga bangarori daban daban.

‘Yan arewacin Najeriya, da ‘yan kabilar Igbo dake zaune a kudancin Najeriya, a yankin na kabilar ta Igbo, na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da batun lkafa kasar Biafra da kuma batun da matasan aewacin Najeriya suka yin a cewa ‘yan kabilar ta Igbo, su bar arewacin Najeriya, na da watani uku.

Bisa tattaunawar da wakilin muryar Amurka yayi da wasu ‘yan kabilar Igbo da ‘yan arewa ya nu na da cewa akwai bukatar daukar matakai dake cike da hikima da hankali domin a samu kaiwa da warware al’amura a cikin ruwan sanyi.

Cyril Okeke, wani dan kabilar Igbo cewa yayi abinda ke faruwa a yanzu ya isa haka yakamata al’umar Igbo, su daina kiran Biafra, domin samun zaman lafiya gaskiya mu bamu son ‘yan arewa su bar yankimu haka kuma bamu son ‘yan uwanmu Igbo su bar arewacin Najeriya.

Shi kuwa Uche, cewa yayi yana goyon bayan cewa duk ‘yan kabilar ta Igbo, dake zaune a arewacin Najeriya, dasu dawo gida yayin da ‘yan arewa su kuma da suke gudanar da harkokinsu a kudanci yankin na kabilar Igbo, su koma yanke sun a arewacin kasar domin acewarsa suna goyon bayan kafar kasar Biafra.

Alhaji Musa Saidu cewa yayi a wasu wurare da ake furta cewa tilas ne Hausawa su tafi yana tsorata mutane yakamata Igbo, su san cewa Hausawa ma mutane ne.

Shima Alhaji Shehu, cewa yayi suna cikin fargaba dare da rana na rashin sani abinda zai iya faruwa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG