Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yankewa Wani Soja Hukuncin Kisa Saboda Ya Kashe Dan Boko Haram Da Baya Dauke Da Makami


Kotun Soja A Maiduguri
Kotun Soja A Maiduguri

Wasu Sojojin Najeriya su gamu da hukuncin akan laifuffuka daban daban da suka aikata da ya sabawa tsarin mulkin Najeriya

Wata kotun Soja mai zama a Maiduguiri ta yankewa wasu Sojoji biyar hunkunci cikin harda wanda aka yankewa hukuncin kisa ga wani jami'in Soja dake da mukamin kofur Hillary Joel, sakamakon kisan da kotun tace ya aikata inda ya kona wani mutun da wuta har lahira.

Mai shara’a Brigediya janar O, Adeniyi, yace kofur Hillary Joel, ya aikata wannan laifi ne lokacin da suka je gudanar da wani aiki a garin Dambua, inda suka shiga gidan wani mutun domin gudanar da bincike suka gano bindiga da man fetur da dai wasu abubuwa agidan wannan mutumin binciken da suka gudanar tare da rakiyar ‘yan civilian JTF.

Brigediya Adeniyi, yace jami’in Sojan ya aikata abinda ya aikata ne lokacin yana kurtun Soja, kuma batare da gudanar da bincike ba inda ya bankawa mutumin wuta wanda ake kira Wobi Lawan, amma aka fi sani da suna “Chemical” wanda kuma wutar da aka banka masa shi yayi sanadiyar mutuwarsa.

Da yake yanke hukuncin Janar Adeniyi, yace bayan bincike da kotun ta gudanar ta kuma samesu da laifi ta yankewa kofur Hillary Joel, hukuncin kisa Chima Daniel, daurin shekaru goma sha biyar (15) a gidan yari wanda aka zarga shima da laifin kisan kai a garin Zabarmari dake karamar hukumar Jere, a jihar Borno, an dai zargi Chima Daniel, da kisan kai ga wani yaro da ake kira Yakubu Isa, wanda ya azabtar dashi da bulala da barkono a bias zargin cewa yaron ya sace masa wayar hannu abinda yayi sanadiyar mutuwan yaron mai shekaru goma sha uku (13).

A cigaba da hukuncin kotun kuma ta ragewa wani da ake kira Aliyu Abdu, mukamin daga kofur zuwa kurtu sakamakon cin zarafin wasu yara uku da yayi da ya nakadawa duka. Wanda kuma yin hakan ya sabawa tsarin dokokin Najeriya, wadannan yara dai sun hada da Yakubu Isa, Baballe Mustapha da kuma Sani Mustapha, duk mazauna kauye Zabarmari a karamar hukuma Jere dake jihar Borno.

Shara'ar da aka yankewa Sojojin sai majalisar koli da Sojojin Najeriya ta rattaba hannu kafin a aiwater dashi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:22 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG