Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaki Da Boko Haram: An Kaddamar Da Shirin “Operation Gama Aiki.”


Wasu sojojin Najeriya da kayan aiki

A wani al'amari mai nuna alamar an shiga wani babi mai sarkakkiya a yakin da ake yi da Boko Haram, sojojin Najeriya sun kaddamar da shirin "Operation Gama Aiki."

Baya ga shirin “Operation Lafiya Dole,” an sake kaddamar da wani shirin kuma mai suna “Operation Gama Aiki” a jahar Borno. Wannan, ga dukkan alamu, na da nasaba da shirin gama yaki da Boko Haram da sojojin ke so su nuna ma jama’a cewa abin da su ka sa gaba Kenan yanzu a babin da aka shiga a wamnnan yakin.

Da ya ke bayani ma wakilinmu a Maiduguri, Haruna Dauda, Shugaban Horaswa da kuma Ayyuka na Rundunar Sojin Sama Ta Najeriya Air Vice Marshal Ahmed Abdullahi, ya ce har yanzu za a cigaba da shirin Zaman Lafiya Dole a yayin da kuma ake aiwatar da “Operation Gama Aiki.”

Ya ce a karkashin shirin “Operation Gama Aiki,” da sojojin Najeriya da na makwabtan kasashe ne za su danna cikin dajin Sambisa daga fuskoki daban-daban. Ya ce ana cigaba da samun nasarori sosai a yakin da ake yi da ‘yan Boko Haram din.

Ga wakilnmu a Maiduguri Haruna Dauda da cikakkiyar hirar:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG