Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaki Da Boko Haram: Rundunar Soji Zata Sake Lale


Sojojin Najeriya (File Photo)

Rundunar sojin Najeriya ta ce za ta bullo da sabon salo wajen fafatwa da kungiyar Boko Haram, bayan umurnin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba ta jiya Alhamis cewa, ta kassara kungiya mai tsattsauran ra'ayin addinin cikin watanni uku masu zuwa.

Mukaddashin jami'in yada labarai na Ma'aikatar Tsaron Najeriya Kanar Rabe Abubakar, shi ne ya yi wannan bayanin, bayan da Shugaba Buhari ya rantsar da sabbin manyan jami'an soji jiya Alhamis a Abuja.

Sabbin manyan jami'an sojin sun hada da Janar Abayomi Gabriel Olonishakin, Hafsan Hafsoshin Tsaron Najeriya; Laftana-Janar Tukur Yusuf Brutai, Hafsan Dakarun Kasa na Najeriya; Vice Admiral Ibok-ete Ekwe Ibas, Hafsan Dakarun Sojin Ruwa; Air Marshal Sadique Abubakar, Hafsan Dakarun Sojin Sama.

Kanar Abubakar ya ce a shirye sojojin su ke su kara kaimi don ragargaza Boko Haram.

"Wannan umurni ne na Shugaban kasa, kuma sojojin Najeriya sun tsara duk hanyoyin da za su bi, wajen ganin bayan Boko Haram a wannan kasar. Kuma na yi imanin cewa za mu iya cimma hakan kafin cikar wa'adi muddun akwai kayan aiki, wanda kuma munsan akwai su. Mu na duk abin da mu ke iyawa wajen ganin cewa mun cimma hakan cikin wa'adin na watanni uku," a cewar Abubakar.

To saidai masu suka na jafa ayar tambaya kan wa'adin na tsawon watanni uku. Sun yi nuni da cewa ai su wadannan sojojin ne su ka yi ta gwabzawa da Boko Haram na tsawon akalla shekaru 5 ba tare da dakile su ba.

XS
SM
MD
LG