Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahamat Daoud Shi Ne Sabon Shugaban Kungiyar Boko Haram - In Ji Shugaba Deby


FILE - The President of Chad Idriss Deby.
FILE - The President of Chad Idriss Deby.

Shugaba Idris Deby na kasar Chadi yace kungiyar Boko Haram ta Najeriya ta yi sabon shugaba.

Wannan furuci na shugaban Chadi yana zuwa ne makonni kadan a bayan da sanannen shugaban kungiyar, Abubakar Shekau, ya kasa bayyana cikin faifan bidiyo na baya-bayan nan da kungiyar ta fitar, abinda ya sa aka fara rade-radin ko wani abu ya same shi ne.

A tattaunawar da yayi da 'yan jarida a lokacin bukin cikar shekaru 55 da samun 'yancin kan kasar Chadi daga Faransa, shugaba Deby yace "akwai wani mai suna Mahamat Daoud wanda aka ce ya maye gurbin Abubakar Shekau, kuma yana son yin tattaunawar sulhu da gwamnatin Najeriya."

Shugaban na Chadi ya kara da cewa a yanzu dai an riga an "sare kan" kungiyar Boko Haram a matakan murkushe ta'addancin da kasashen yankin suka dauka.

Shugaba Deby ya ce, "akwai wasu gungu-gungu na 'yan Boko Haram marasa yawa dake warwatse yanzu haka a yankin bakin iyakar Najeriya da Kamaru. Muna da sukunin da zamu iya murkushe Boko Haram. Wannan yakin ba zai dauki wani lokaci ba, rundunar kasashen yanki zata iya gamawa da su nan da karshen shekarar nan."

XS
SM
MD
LG