Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaki da Cin Hanci da Rashawa Zai Tabbatar da Rayuwar Matasa - Shugaba Buhari


Shugaba Buhari

Yayinda yake yiwa shugabannin daliban jami'o'in Najeriya yace yakin da gwamnatinsa keyi da cin hanci da rashawa zai kare rayuwar matasa.

Yau shugaba Buhari ya gana da matasa daga jami'o'in Najeriya a Abuja inda ya fada masu cewa yakin da gwamnatinsa take yi da cin hanci da rashawa domin tabbatar da rayuwarsu ne da cigabansu.

A cikin jawabin da ya yiwa kungiyar daliban jami'o'i da ake kira National Association of Nigerian Students ko NANS a takaice da suka yi maci zuwa fadarsa ta Aso Rock Villa saboda nuna goyon bayansu da yakin da shugaban ke yi, shugaba Buhari yayi masu alkawarin yin duk iyakacin kokarinsa ya ga Najeriya ta zamo kasar da zata kaisu ga cin muradunsu.

Yace duk abubuwan da muke nema abubuwa ne da zasu gyara kasar kuma abun da muke nema ita ce kasa mai kyau, mai adalci da tsare gaskiya inda matasanmu zasu rayu cikin walwala da bege mai kyau-inji Buhari.

Yace mun dukufa wurin gina kasa wadda zata ba kowa daman zama abun da yake son ya zama.

Ina baku tabbaci cewa jin dadinku, walwalarku da lafiyarku su ne suka fi mahimmanci garemu kuma nan ba da dadewa ba zaku ga abubuwan da muka yi maku alkawari, a cewar shugaban.

Yace lokacin zabe alkawari muka yi amma yanzu zamu aikata alkawuranmu gadan gadan.

Daga bisani daliban sun mika wasu takardu da suka shirya da ake kyautata zato suna kunshe ne da wasu shawarwari.

XS
SM
MD
LG