Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaki Da Nuna Banbancin Launin Fata: Kamfanin Unilever Zai Daina Fifita Launin Fari


Wasu kayan shafe shafen canza launin fata na Unilever

Zanga zangar rashin amincewa da nuna banbancin launin fata, wadda kungiyar gwagwarmayar kare bakake ta Black Lives Matter ta jagoranta, biyo bayan mutuwar George Floyd a Amurka, ta yi tasiri har a wuraren da ba a zata -- alal misali, kamfanin yin nau’ukan man sa fatar mutun ta zama fara, wanda ke kasuwa sosai musamman a Indiya da sauran kasashen Asiya, ya fara tunanin canza lafazin tallarsa.

Katafaren kamfanin na Unilever ya yi shelar cewa zai canza sunan sanannen rukunin man nan nasa na Fair and Lovely (wato Fara Son Kowa), wanda tun da dadewa ake cukar wannan kalamin da cewa ya na yada kalaman kaskanci na cewa farar fata ta fi ban sha’awa.

“Mun lura cewa amfani da kalmar “fari”, ‘haske’ da makamantan haka na nuna kamar wata kala guda ce kawai ke iya kyau wanda mu na ganin hakan ba daidai ba ne kuma mu na so mu gyara wannan kuskuren,” a cewar Sunny Jain, shugaban sashin kayan inganta kyan ciki na kamfanin kayan shafe-shafen gyara jiki na Unilever a wata takardar shela a jiya Alhamis.

Fairness Cream ads
Fairness Cream ads

Wasu kayan 'bilicin.'

Man kara farin fata na Fair and Lovely wanda kamfanin na Unilever ke yi ya kasance daya daga cikin mayukan da aka fi saye a Indiya, ta yadda ma akan aje shi a wuri na musamman a kanti, kuma ya kasance sananne ba ma kawai a birane ba, har ma da kauyuka.

‘Yan gwagwarmaya, wadanda tun dama ke yin tir da wannan man shafawa saboda dada kaskantar da bakar fata da yak e yi, sun yi lale marhaban da wannan matakin ta kamfanin ya dauka a matsayin farkon gyara, amma suna ganin canza sunan man kawai ba zai wadatar ba.

“Wannan wata babbar nasara ce gare mu,” a cewar Kavitha Emmanuel, Wadda ta kaddamar da fafatukar nan mai suna “Dark is Beautiful,” wato “Bakar Fata Na Da Kyau,” wadda ke yaki da shafe-shafen canza launin fata, a 2009.

Kayan shafe shafen canza launin fata zuwa fari na cinikin miliyoyin daloli a nahiyoyin Afurka da Asiya, ta yadda kamfanonin kayan kwalliya da dama ke ta ke rige-rigen shiga irin wannan kasuwancin wanda ya ta’allaka kan ra’ayin nan na cewa farar fata ta fi kyau -- wanda wannan ra’ayin ya samo asali ne daga mulkin mallakar da aka yi wa nahiyoyin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG