Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaki da ta'adanci da keta hakkin mutane a Afirka


Kwamitin kare hakkin bil Adam na majalisar dokokin Amurka yana sauraren shaidu
Kwamitin kare hakkin bil Adam na majalisar dokokin Amurka yana sauraren shaidu

Wakilan majalisar dokokin Amurka wadanda suke nazarin irin barazanar ta'addanci a Afirka, jiya Talata sun bayyana damuwa cewa, Amurka tana kauda kai kan keta 'yancin Bil'Adama da rashin adalci da shugabannni a yankin suke yi, muddin dai suna bada tallafi a yaki da ta'addanci.

Mukaddashiyar sakataren harkokin wajen Amurka Linda Thomas- Greenfield, ta fadawa kwamitin kula da harkokin waje a majalisar dattijai cewa kasashe da suke nahiyar Afirka sassa da suka gaza kuma tilas ne a fuskanci wannan matsala. Greenfield ta gayawa wakilan kwamitin cewa, kungiyoyin 'yan ta'adda suna samun magoya baya ta wajen kwadaita musu kudi.Domin raddi kan irin wannan mataki, tace tilas ne gwamnatoci suyi amfani da dukkan wata dama da suke da ita wajen samar da ilimi da koya musu sana'o'i.

Amma Senata Ben Cardin, ya bayyana damuwar cewa, hukumomi a Washington, suna kyale gwamnatoci da suke keta 'yancin Bil'Adama da rashin adalci, mudddin dai suna da amfani wajen yaki da ta'adanci. Senatan yace

Alal misali a Habasha ko Ethiopia,an yi zaben 'yan majalisa inda babu dan hamayya daya da aka zaba,kuma sojojin kasar sun kashe daruruwan masu zanga zanga, a Cadi, an kama sojojin kasar masu yawa saboda kawai sun ki su zabi shugaban kasar, a Somalia,akwai rahotannin cewa,hukumomi suna amfani da yara wajen yi musu leken asiri,a Najeriya da Kenya, akwai rahotannin sojoji suna kashe mutane ba tareda an yanke musu shari'a ba. Inji Senata Cardin.

Sakatariya Greenfield tace, a duk irin wadannan yanayi, gwamnatin Amurka tana tur da Allah wadai kan irin wadannan matakai,duk da haka tace, a shirye Amurka take sosai wajen aiki da kawayenta domin ganin bayan ta'adanci.

XS
SM
MD
LG