Accessibility links

Taron yaki da ta'adanci a Najeriya gwamnati ce ta shirya domin a fadakar da kawunan mutane game da yakin dake gudana jihohi uku na arewa maso gabashin Najeriya.

Yayin da take bayani darektan canza dabi'a Fatima Akilu ta ce labarun da 'yan jarida ke yayantawa ba labaru ba ne da suka kunshi gaskiya. Ta ce mutanen dake zaune a wuraren da ake farautar 'yan Boko Haram suna yin murna da matakan da sojoji suka dauka. Ta ce yawancin 'yan tawayen an fatattakesu kuma wuraren dake hannunsu da yanzu sun koma hannun gwamnati. Ta ce idan katse hanyar sadarwa zata taimaka a cimma zaman lafiya mutane sun yi na'am da hakan. Ta ce ita ma kanta ta kai ziyara zuwa Maiduguri inda ta ga mutane na raywarsu ba tare tsangwama ba daga dakarun JTF. Yara suna zuwa makaranta ba tare da samun wata matsala ba. Ta ce mutane basa tsoron komi.

Da aka tambayeta cewa idan mutane basa tsoro to me zata ce kan rahoton Majalisar Dinkin Duniya da ya ce mutane kusan dubu shida ne suka yi gudun hijira zuwa Jamhuriyar Nijar. Ta ce JTF na iyakacin kokarinta ta kare rayukan mutane. Don haka idan wasu fada ya ritsa da su to ba da gangan ba ne kuma basu da yawa. Amma Dr. Uma Azar dan asalin jihar Adamawa cewa ya yi ana samun asarar rayuka maimakon karesu.Ya bada misali da mata masu juna biyu da suka mutu su da 'ya'yansu domin basu samu sun je asibiti ba sabili da dokar hana fita. A nashi ra'ayin dole ne gwamnati ta bada diyya ga iyalan wadanda suka rasa 'yan'uwa sabili da dokar da ta kutuntawa mutane musamman idan manufar gwamnati ta haddasa mutuwar mutane. Ya kara da cewa idan sabili da hare-hare ne ya sa gwamnati ta kakabawa Adamawa dokar ta baci to kamata ya yi ta aiwatar da dokar a birnin Abuja domin, inji shi, hare-haren da ake kaiwa kan Abuja sun fi na Adamawa.

Daga bisani tsowon shugaban kasar Najeriya Janaral Gowon ya ce kada 'yan Najeriya su kwatanta addinin Musulunci da abubuwan da 'yan Boko Haram ke yi. Ya ce abun da suke yi ba shi ne Musuluncin da shi ya sani ba. Ya ce Musulmai mutane ne masu son zaman lafiya da kowa.

Nasiru Adamu El-Hikaya na da karin bayani.

XS
SM
MD
LG