Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaki Na Iya Barkewa a Fagen Cinayyar Duniya


Shugaban Amurka Donald Trump

Barazanar yaki a fagen cinayyar duniya na dada karuwa yayin da kasar Amurka da tarayyar Turai ke ta gasar maka ma juna haraji.

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar maka harajin kashi 20% kan motocin da ke shigowa daga Turai, a matsayin martanin harajin da kasashen Turai su ka saka kan kayakin da ke shigowa daga Amurka.

Jiya Jumma'a, wato kwana guda, bayan da sabon harajin na kasashen Turai ya fara aiki, Trump ya rubuta ta kafar twitter cewa, "muddun ba a gaggauta dakatar da wannan haraji da kuma tarnakin ba, za mu maka harajin kashi 20% kan dukkan motocinsu da ke shiga Amurka. A rika yi a nan Amurka!"

Kwararru sun ce irin wannan harajin ka iya gurgunta tattalin arzikin Amurkar da Turai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG