Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

YAJIN AIKI: Kotunan Adamawa Sun Kusa Zama Kufai


Wani Lauya da wanda yake karewa a kotu

Fiye da watanni hudu ke nan da kungiyar ma'aikatan kotunan Najeriya ta kirawo 'ya'yanta shiga yajin aiki.

Yajin aikin ma'aikatan kotuna ya jefa lauyoyi da wadanda ke jiran hukunci cikin wani mawuyacin hali.

Kotuna a jihar Adamawa suna neman komawa kufai saboda wata da watanni ke nan babu kowa cikinsu. Ma'aikatan sun shiga yajin aikin ne a fafaitikar da suke yi na neman a baiwa fannin shari'a daman cin gashin kansa ta hanyar basu kudadensu kai tsaye ba tare da rage murya gaban gwamnatoci ba.

Tuni wasu jihohin suka rungumi shirin kamar yadda gwamnatin tarayya tayi.Rashin aiwatar da shirin a jihar Adamawa ya sa yajin aikin ya cigaba lamarin da ya haifar da cunkoso a ofisoshin 'yan sanda inda suke rike da wadanda suka aikata laifuka. Yanke shari'a ga wadanda suke jiran hukunci shi ma ya samu cikas.

Mutane na ganin dole ne a dauki matakin gaggawa. Alhaji Muhammad Oscar yace babu kotu talakawa kuma suna nan jibge a hannun 'yansanda. Su ma 'yansandan sun gaji.

Kungiyar ma'aikatan kotunan Najeriya tana zargin wasu gwamnatocin jihohi da nuna halin ko in kula game da yajin aikin. Shugaban hadakar ma'aikatan kotunan Najeriya reshen jihar Adamawa yana zargin gwamnatin jihar da yin kunnen shegu game da halin da yajin aikin ya jefa jama'a ciki. Yace gwamnonin da suka mutunta shari'a da sanin darajar mutanensu sun aiwatar da abun da dokar Najeriya ta tanada. Sun sakarwa kotunansu mara amma banda Adamawa.

Lauyoyi su ma sun nuna bacin ransu. Barrister Abubaka Baba Kano shugaban kungiyar lauyoyin jihar Adamawa yace yajin aikin ya jefasu cikin halin tsaka mai wuya. Yace duk abun da ya jibanci shari'a ya tsaya tsit kama daga wadanda suke kurkuku suna jiran hukunci da wadanda 'yansanda suka tsare suna jiran su gurfanar dasu gaban kotuna..

Gwamnan jihar ya mayarda martani ta bakin kakakinsa Mr. Peter Elisha. Ya bayyana irin matakan da gwamnatinsa ta dauka akan lamarin. Batun samarma alkalai motoci gwamnati tayi. Batun gyara kotuna gwamnatin tayi. Amma batun samun gashin kansu sai majalisa ba batun gwamna shi kadai ba ne. Dole a samu doka daga majalisa da zata bada izini.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:00 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG