Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yakin Neman Zaben Shugabancin Najeriya Ya Zafafa


Yankin neman zabe

A Najeriya ya yin da ya rage ‘yan kwanaki kaddamar da babban zaben, a gefe guda kuma yan takarar kujerar shugabancin kasar musamman ‘yan jam’iyyar APC Muhammadu Buhari da na PDP Atiku Abubakar suna ta zafafa yakin neman zabensu i ta hanyar ziyartar jihohin kasar.

Lokacin da shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya je yakin neman zabe jihar Gombe, shi kuwa wazirin Adamawa na jam’iyyar PDP makwabciyar jihar Bauchi ne ya ziyarta domin neman kuri’a.

Shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada wa ‘yan Najeriya zai tabbatar ya ci gaba da rike amana idan aka sake zaben shi.

Har ila yau a jihar Gomben, jam’iyyar APC ta yi babban kamu inda shugaban kwamitin yakin neman zaben dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP Alhaji Bala Bello Tinka, ya ce ya fice daga jam’iyyar yakoma APC, inda ya yi waiwaye adon tafiya a jawabin daya gabatar.

Shi kuwa wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar, a jawabin yakin neman zabensa da ya gabatar a Bauchi ya bukaci ganin jami’an tsaro ne da kada su tsunduma kansu a siyasa, da farko ya bukaci jama’ar jihar Bauchi da su fito don kada kuri’a wa jam’iyyar PDP.

Shugaban kwamitin yakin zaben Atiku Abubakar a shiyyar arewa maso gabas, gwamnan Gombe Ibrahim Hassan Dan Kwambo ya bukaci yan uwansa yan jihar Bauchi da su kada kuri’arsu ma jam’iyyar PDP.

Domin karin bayani saurari rahotan Abdulwahab Muhammad.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG