Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Adawa A Uganda Sun Ki Yarda Da Sakamakon Zaben Ranar Lahadi


Madugun 'yan adawa a Uganda, Bobi Wine

Jam’iyyar adawa akasar Uganda ta su dan takara Bobi Wine, a jiya Lahadi ta ce zata kalubalanci sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi.

“Muna da shaidu da kuri’un bugi da ma wasu abubuwa da suka faru lokacin zaben, muna kuma kokarin hada kansu a waje daya, don bin dokoki da shari’a ta tanadar, zamu kalubalancin murdiya da aka yi.”

A cewar Mathias Mpuuga na jam’iyyar National Unity Party, lokacin ganawa da manema labarai jiya Lahadi. Kwana daya ke nan da kwamishina zabe ya tabbatar da Shugaba Yoweri Museveni a matsayin wanda ya lashe zaben na 2021.

Tunda ya dare kan Karagar Mulkin kasar Uganda a shekarar 1986, Museveni mai shekaru 76 a duniya, ya shugabanci kasar kai tsaye, ya kuma yi watse da kiraye-kiraye da ake yi na cewar an yi magudi a zaben, wanda ya kada dan takara Wine, mawaki mai shekaru 38 a duniya, kuma dan majalisa.

Biyo bayan sanarwar jam’iyyar Adawa Jiya Lahadi, wadda ta ce tun bayan sanar da sakamakon zaben a wata zanga-zanga an tabbatar da mutuwar mutum 2.

Amurka da Burtaniya sun nuna damuwarsu akan sakamakon zaben, wanda aka rufe duk wasu kafafen sadarwar yanar gizo a kasar gabanin gudanar da shi.

Wine ya ce, jami’an shi suna da hotunan bidiyo na magudi da aka tabka, amma basu iya watsa su ta kafar yanar gizo ba saboda rashin intanet din a kasar.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG