Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Adawa Na Shirin Shiga Gwamnatin Nijar


Shugaba Mahamadou Issoufou, wanda jam'iyyarsa ta PNDS-Tarayya ta ke shirin gayyatar jam'iyyun adawa su shigo cikin gwamnati

Kotun tsarin mulkin Nijar ta share fagen hakan a bayanda ta amsa ma firayim ministan kasar cewa 'yan adawa su na iya shiga gwamnati ba tare da keta tsarin mulkin kasar ba

Jam'iyyun adawa na Jamhuriyar Nijar su na shirin shiga cikin gwamnatin hadin kan kasa wadda aka ce shugaba Mahamadou Issoufou da jam'iyyarsa ta PNDS-Tarayya suke tunanin kafawa tare da gungun 'yan adawa.

A makon jiya ma, sai da firayim ministan Nijar din ya tuntubi kotun tsarin mulki ta kasa a kan ko 'yan adawa su na iya shiga cikin gwamnatin hadin gambiza ta kasa ba tare da sun saba tsarin mulkin kasar ba. Kotun ta ba shi amsa da cewa, jam'iyyun adawa su na iya shiga cikin gwamnati a dama da su.

Wani kakakin gamayyar jam'iyyun adawar a Nijar, Alhaji Doudou Rahama, yace su na iya shiga cikin gwamnatin idan har shugaban kasa zai cika sharrudan da suka gindaya. Yace yin hakan ba zai nkawar da nauyin dake wuyansu na kare muradun 'yan kasa da tabbatar da cewa gwamnati tana aiki ma jama'a ba.

'Ya'yan jam'iyyar PNDS-Tarayya dake mulkin kasar, sun yaba da abinda suka bayyana a zaman hangen nesa na shugaba Mahamadou Issoufou wajen gayyato 'yan adawa cikin gwamnatinsa. Memba na jam'iyyar, Alhaji Asoumana Muhammadou, yace shigar da 'yan hamayyar zata kawar da irin rigingimun da aka yi ta gani cikin gwamnatocin kasar da aka yi shekaru 20 da suka shige.

Ga cikakken bayanin da wakilin sashen Hausa, Abdoulaye Mamane Ahmadou, ya aiko daga birnin Yamai.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG