Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Adawa Sun Jinkirta Nuna Bijirewar Rantsar Da Raila Odinga


Jagoran 'yan adawar Kenya Raila Odinga

Da alamar 'yan adawar Kenya, wadanda su ka so rantsar da Raila Odinga a matsayin nuna bijirewa ga gwamnati, sun zabi bi a hankali bayan da Attoni-Janar din kasar ya ce hakan na iya janyo ma Odinga dauri

‘Yan adawar kasar Kenya sun jinkirta shirinsu na kaddamar da shugabansu Raila Odinga, wanda ya kaurace ma zaben da aka yi a watan Oktoba, a cewar jam’iyyarsu a jiya Lahadi.

Ada, hadakar NASA ta yi shirin kaddamar da Odinga a matsayin Shugaban kasa na kwatance kawai a gobe Talata, zagayowar ranar samun ‘yancin kasar Kenya, makonni biyu bayan da aka rantsar da Shugaba mai ci Uhuru Kenyatta na wa’adi na biyu.

Hadakar NASA ta ce an yanke wannan shawarar ce bayan tuntuba da tattaunawar da aka yi da wasu magaba a ciki da wajen kasar, ba tare da ambatar sunan ko daya daga ciki ba.

Attoni-Janar din Kenya ya fadi a makon jiya cewa duk wani bukin kaddamar da Shugaba na kwatance na iya janyo tuhumar cin amanar kasar ga Odinga, wanda laifin hakan a kasar Kenya shi ne kisa.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG