Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Congo: ‘Yan Adawa Sun Yi Ikrarin Samun Nasara a Zaben Raba Gardama


Wani Mutum Rike Da Wani Allo Da Ke Nuna Cewa "Kasar Congo Ba Mallakar N'guesso Ba Ce."

Wani jagoran 'yan adawa na ikirarin nasara a kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka kada jiya Lahadi a Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo, saboda abin da ya kira rashin fitowar jama'a sosai.

Shugaban Jam'iyyar Union for Democracy and Republic, Guy Kinfoussia Romain, ya ce mutane Congo sun yi aiki da kiraye-kirayen 'yan adawa na su kauracewa zaben saboda kuri'ar jin ra'ayin jama'ar wata haramtacciyar hanya ce ta taimaka ma Shugaba Denis Sassou-N’guessou ya dore bisa gadon mulki.

Shugaba N’guesso ya shugabanci kasar ta Congo a matsayi daban-daban a mafi yawan tsawon shekaru 36 da su ka gabata.

Kundin tsarin mulkin kasar na yanzu ya haramta masa shiga zaben 2016 saboda shekarunsa sun dara 70.

Amma N’guesso, dan shekaru 71 da haihuwa ya bukaci a kada wannan kuri'a ta jin ra'ayin jama'a kan yiwa kundin tsarin mulkin kwakwarima ta yadda zai samu yin takarar wa'adi na uku.

Romain ya ce kashi 3% ne kadai su ka kada kuri'ar jin ra'ayin jama'ar ta jiya Lahadi. Ya ce ya kamata al'ummar duniya ta agaza ma mutanen Congo wajen hana Shugaba N’guesso canja kundin tsarin mulkin kasar.

Romain ya ce dole ne Shugaba N’guesso ya sauka ya kuma shirya sabon zabe.

To amma wani jami'in jam'iyyar Congo Congolese Labor Party, jam'iyyar da ke mulkin kasar ya gayawa Muryar Amurka cewa 'yan kasar ta Congo ne su ka bukaci a yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, amma ba Shugaba N’guesso ba.

Mai magana da yawun jam'iyyar da ke mulki, Serge Michel Odzoki, ya ce gwamnati na maraba lale da zanga-zangar da ake yi saboda wani bangare ne na tsarin dimokaradiyya matukar dai ba su rikida sun zama tashin hankali ba.

XS
SM
MD
LG