Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Adawan Venezuela Sun Ki Amincewa da Sakamakon Zaben Ranar Lahadi


Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro yana jawabi bayan sakamakon zaben gwamnonin jihohi 23 dake kasar
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro yana jawabi bayan sakamakon zaben gwamnonin jihohi 23 dake kasar

Gamayyar kungiyoyin 'yan adawan kasar Venezuela sun yi watsi da sakamakon zaben gwamnonin da gwamnatin ta gudanar ranar Lahadin da ta gabata inda 'yan socialist suka lashe jihohi 17 cikin 23

Gamayyar kungiyoyin ‘yan adawan Venezuela sun ki amincewa da sakamakon zaben gwamnonin da aka yi ranar Lahadi, wanda jam’iyyar mai mulki ta Socialist ta sami lashe jihohi 17 cikin jihohi 23 na kasar.

A cewar daraktan kamfen din jam’iyyar DUR, Gerardo Blyde, “Bamu amince da kowanne sakamako ba a wannan lokaci. Muna fuskantar wani yanayi a wannan kasar.” ya kuma yi kira da a sake kidayar kuri’un zaben.

Jam’iyyun adawar, da aka yi hasashen cewa zasu lashe a kalla rabin jihohin kasar, sun sami guda biyar kacal, yayin da har ya zuwa yau Litinin ake ci gaba da kidayar kuri’u a gabashin jihar Bolivar.

Shugaban kasa Nicolas Maduro ya yaba da sakamakon zaben kuma ya ta’allaka nasarar akan akidar “Chavismo” ta tsohon shugaban kasar, marigayi Hugo Chavez.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yabawa mutanen kasar Venezuela, saboda abinda ta kira “karfin hali da kudirin da suka nuna da kumaamfanin da suka yi da damarsu da kundin tsarin mulki ya basu” na fita su kada kuri’unsu.

Sai dai Amurka ta nuna jin takaicin ganin cewaba a saurari muryoyin ‘yan Venezuela din ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG