Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Awaren Basque Ta ETA Sun Yi Watsi Da Fafutikar Ballewa Daga Spain


Shugabannin kungiyar Basque ta ETA yayinda suke neman gafara wurin al'ummar kasar Spain dangane da shekaru 60 da suka yi suna kashe mutane a fafutikarsu

Bayan shekaru 60 da suka yi suna fafutikar neman kafa wata kasa daban daga Spain 'yan kungiyar awaren Basque ta ETA sun wargaje fafutikarsu sun kuma nemi gafara

Kungiyar yan awaren Basque ta ETA a hukumance ta wargaje bayan shekaru 60 kuma ta yi watsi da fafitukar neman a kafa kasar Basque a Arewacin kasar Spain da kuma kudancin Faransa.


Wata jaridar Spain ta El Diario ce ta buga wata wasikar ragowar shugabannin kungiyar ETA a kan shafinta na yanar gizo


Wasikar tana cewar, kungiyar ETA ta ayyana kawo karshen ayyukanta na shekaru da sauran kungiyoyi, ta kuma kawo karshen tafiyarta, ETA ta wargaje kwata kwata ta kuma ayyana kawo karshen harkokin siyasarta.


Sai dai wasikar tace fada tsakanin kasar Basque da Spain da kuma Faransa zai ci gaba.


Ministan harkokin cikin gidan Spain Juan Ignacio Zoido yace gwamnati zata ci gaba da farautar wadanda ta kira yan ta’addar Basque.


Yace ba zasu samu abin da zai basu damar ayyana abin da suka kira shirin wargazawa ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG