Accessibility links

'Yan bindiga sun sace wani baturen Jamus a Nigeria

  • Jummai Ali

Mutane a Kano Nigeria

'Yan Bindiga a Nigeria sun sace wani baturen Jamus Injiniya a Kano arewacin Nigeria inda a makon jiya tashin bama bamai suka kashe akalla mutane dari da tamanin da takwas

Yan bindiga a Nigeria sun sace wani baturen Jamus, injiniya a birnin Kano dake arewacin kasar, inda tashe tashen bama bamai a makon jiya suka kashe akalla mutane dari da tamanin da biyar.

Jiya Alhamis, kwamishinan yan sanda jiyar yace, saida aka sawa Bajamushe ankwa kafin a tura bayan wata mota, aka yi awon gaba dashi. An sace su a wani wuri da suke aikin kwangila wa wani kamfanin Nigeria.

Yan sanda sunce suna binciken al'amarin, suma jami'an ma'aikatar harkokin wajen Jamus sunce suma suna nazarin al'amarin.

Kamfanin Dantata da Sawoe da mutumi yake yiwa aiki bace komai ba tukuna.

An dai sace wannan Bajamushe ne, a yayinda sabon shugaban yan Sandan Nigeria ya fara aiki, a yayinda kuma ake fama da karuwar tarzoma wadanda aka dora laifi aukuwarsu akan kungiyar yan yaki sa kai ta Boko Haram.

Jiya Alhamis ma wani bam ya tashi a wani wurin shiga motoci a watan unguwar da Kirista suka fi yawa a cikinta a Kanon. Rahotanin su baiyana cewa mutane biyar ne suka ji rauni.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG