Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An sake kai wani hari kan ofishin 'yan sanda a birnin Kano


Wani yaro yana tsaye kan motar 'yan sanda aka kona

Wadansu ‘yan bindiga sun sake kai sabon farmaki a Kano, inda a a na jiyan ma suka sake abkawa wata ma’aikatar ‘yansanda. Wannan harin yana zuwa bayan na makon jiya da aka kai da ya hallaka mutane sunfi da 180.

Wasu ‘yan bindiga sun sake kai sabon farmsaki a Kano, inda a a na jiyan ma suka sake abkawa wata ma’aikatyar ‘yansanda. Wannan harin yana zuwa bayan na makon jiya da aka kai da ya hallaka mutane sunfi 180.

Wadansu shaidu sunce wadanan ‘yan bindigar sun abkawa chaji-ofishin ‘yansandan Sheka ne, wata unguwa mai tarin gidaje da jama’a. bayanda suka umurci mutanen unguwar da su ja da baya ne, masu kai farmakin, wadanda ke tafe suna kabbarar “Allahu Akbar”, suka soma bude wuta akan wurin.

Kungiyar Boko Haram dai tace itace ta kai wancan harin na ranar jumu’a da ya kashe mutane 185, wanda bayansa ne shugaba Goodluck Jonathan ya sake maimaita lasar takobin cewa sai ya ga bayan ‘yan kungiyar. Izuwa yanzu dai ba a samu wani cikakken bayani akan ko anyi asaran rayukka a a cikin farmakin na jiya ba, kuma har yanzu ba wata kungiyar da ta fito tace itace ta kai harin.

Shaidu a Kano sun bayyana yau Laraba cewa, babu ko dan sanda daya a kan titi yayinda gungun mutane musamman matasa suka rika shewa kofar caji ofishin 'yan sandan suna tsalle kan motocin 'yan sandan da aka kona. Yayinda aka babbale kofofin dakunan kulle wadanda aka kama dake caji ofis din.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG