Mazauna yankin sun ce sun yan bindigar da makamai masu tarin yawa suna daukar dabaru kafin su abkawa shingen gwamnati a garin.
"Yan bindigan sun kai su dari. Suka raba kansu wurare dabam dabam sannan suka umarci mutane da kowa ya shiga gidajensa kafin suka mamaye shingen da jami’an tsaron gwamnati suka kafa," inji wani mazaunin wurin Mohammed Hirey.
Wani kuma mazaunin yankin, Nur Yusuf Kabale ya bayyana cewa, "Yan tawayen sun yi amfani da manyan bindigogi kirar RPG da kuma wasu muggan bindigogi suna ihu suna cewa 'Allahu Akbar' wato Allah mai girma yayin da suke arrangama da dakarun gwamnati."
Gwamnan Lower Shabelle ya shaidawa Sashen Somaliya na Muryar Amurka cewa yan tawayen sun kaiwa sojojin gwamnatin harin bazata da Magriba daidai faduwar rana amma duk da haka dakarun gwamnatin sun yi sa'ar taresu.