Accessibility links

'Yan bindiga sun kai hari akan yan jam'iyar APC a jihar Rivers

  • Jummai Ali

Yan yakin sa kan yankin Niger-Delta na Nigeria

Wasu 'yan bindiga sun kai hari akan ya jam'iyar APC a jihar Rivers

A yayinda saura kasa da mako guda, a gudanar da zaben gwamnoni a Nigeria, wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su wanene ba, sun kaiwa magoya baya da wasu 'yan takara jam'iyar APC hari a karamar hukumar Omoha ta jihar Rivers.

Ranar Juma'a da dare yan bindigan suka kai wannan hari. Kwamishinan yan sandan jihar ya tabbatar da aukuwar wannan al'amari. Yace shi da kansa yajkaramar hukumar Omoha, ya ganewa idanuwansa abinda ya fari. Yace yanzu haka yan sanda suna sintiri a yankin.

Ya tabbatar wa jama'a a jihar cewa yan sanda zasu kare su.

XS
SM
MD
LG