Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Kai Tagwayen Hare-Hare A Wasu Tashoshin Bincike A Jihar Tilaberry


'Yan Bindiga

‘Yan bindiga sun kai tagwayen hare-hare a wasu tashoshin bincike a garin Makalondi dake jihar Tilabery iyaka da Burkina Faso inda suka hallaka jami’an tsaro tare da kona motoci sannan suka arce da wasu motocin ‘yan sanda.

Lamarin ya faru ne a wajejen karfe 2 na daren jiya laraba wayewar yau alhamis a tashar binciken motcin dakon kaya da ake kira Pont Bascule inda ‘yan bindiga suka bude wuta akan jami’an tsaro abinda ya yi sanadin mutuwar jandama 1 wasu 3 suka ji rauni.

Lokacin kadan bayan haka wasu mahara sun kai farmaki a tashar bincike inda mutun 5 suka rasu cikinsu jami’an Douane 2 da wasu 3 wadanda ba a tantance sub a sakamakon yadda suka kone kurmus.

Haka kuma rahotanni daga garin na Makalondi na cewa ‘yan bindigar sun kona motoci 7 sannan sun arce da motoci 2 na ‘yan sanda hade da wata bindiga kirar M80.

Har Izuwa lokacin aiko da wannan rahoto hukumomi ba su yi karin haske ba dangane da wannan al’amari dake wakana sa’oi kadan bayan da gwamnan jihar tilabery ya bada umurnin rufe gidajen mai da dama a sassan yankin mai fama da masalar tsaro

Saurari cikakken rahoton a cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:39 0:00

Dubi ra’ayoyi

AFCON 2021, Kelechi Iheanacho

"Ku doke daya daga cikin shahararrun koci a duniya", Kelechi Iheanacho, Najeriya bayan sun doke Masar
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:11 0:00
Karin bayani akan Wasanni

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG