Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Malami Guda, Suka Raunata Wani Guda A Borno


Sojojin Najeriya su na sintiri a kusa da wani sansanin kungiyar Boko Haram a Jihar Borno
Sojojin Najeriya su na sintiri a kusa da wani sansanin kungiyar Boko Haram a Jihar Borno

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Borno, Lawan Tanko, yace mutanen biyu da aka kai ma farmaki malaman sakandare ne.

Wasu ‘yan bindigar da ake kyautata zaton cewa ‘ya’yan kungiyar nan ce ta Boko Haram, sun bindige suka kasha wani malami a wani kauyen dake kusa da bakin iyaka a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Borno, Lawan Tanko, ya fada laraba cewa ‘yan bindigar da ake kyautat zaton ‘yan Boko Haram ne sun bi wannan mutumi har zuwa gidansa a wani kauye mai suna Wulgo, suka kasha shi, suka raunata mutum na biyu da suke tare. Mutumin na biyu yana kwance a asibiti.

Kauyen Wulgo yana dab da bakin iyaka da kasar Kamaru.

Wani malami da kuma wani jami’in tsaro sun ce dukkan mutanen biyu da aka harbe malaman sakandare ne. Malamin da kuma wannan jami’in tsaro sun bukaci da a sakaye sunayensu a saboda dalilai na tsaro ko kuma bas u da iznin yin magana kan wannan batun.

Kungiyar Boko Haram dai ta kai wasu munanan hare-hare guda biyu kan makarantun gwamnatin Jihar Yobe a kwanakin baya, inda ta kasha dalibai masu yawa a makarantar Sakandaren gwamnati dake garin Mamudo a kusa da Potiskum, da kuma Kolejin Koyon Aikin Gona ta Yobe dake garin Gujba.
XS
SM
MD
LG