Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane a Kauyukan Kamaru Sun Gudu Don Tsoron ‘Yan Boko Haram


Kauyukan dake bakin iyaka da Najeriya a kasar Kamaru sun zamo kango a saboda kazamin fadan da aka gwabza a tsakanin sojojin Najeriya da 'yan Boko Haram a garin Banki na Jihar Borno

Mutanen dake zaune a kauyukan dake bakin iyaka a yankin arewacin kasar Kamaru, sun hudu sun bar gidajensu a bayan wani kazamin fadan da aka gwabza a tsakanin sojojin Najeriya da mayakan Boko Haram a garin Banki, dake Jihar Borno a tsallaken iyaka.

Wannan kazamin fada da kuma karar harbe-harbe da fashe-fashe a tsakanin sojojin Najeriya da ‘yan Boko Haram sun fiurgiuta jama’a a kauyukan da suke bakin iyaka, musamman ma kauyen Amchide.

Mazauna kauyen suka ce sojojin Najeriya sun yi ta harbi ba kakkautawa, kuma ba tare da la’akari da ko wanene suke harbi ba a lokacin da mayakan Boko Haram suka nemi gudu. Wani dan kasuwa mai suna Halidou Alirou, ya fadawa VOA cewa mutane sun firgita da harbe-harben, har kowa ya waste da gudu zuwa cikin dazuzzukan dake kusa da nan. Yace a dalilin haka ne ya rasa inda matarsa ta shiga, kuma tana yiwuwa wasu ba zasu komo gida da wuri ba.

Rundunar sojojin Najeriya ta yi amfani da sojojinta na kasa da kuma jiragen yaki a wannan farmakin. Wani mutumin kauyen, Ayang Kaina, yace akwai ‘yan Najeriya da dama dake gudu daga wannan fadan da suka ji rauni.

Kaina yace an yi ta harbe-harbe daga ta ko ina, daga cikin motoci, daga jiragen yaki masu saukar ungulu, kuma an lalata gidaje da dukiya mai yawa.

Da yawa daga cikin wadanda suka ji rauni an garzaya da su zuwa asibitoci a kauyukan dake kusa da nan. Wasu mutane biyar da suka ji mummunan rauni kuma an dauke su zuwa Maroua a arewacin Kamaru.

Mayakan da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne sun yi kokarin su gudu zuwa cikin Kamaru dauke da makamansu, amma sojojin Kamaru sun ja daga suka fafata da su.

Ministan tsaron Kamaru, Edgar Alain Mebe Ngo'o, ya kai ziyara wurin ranar alhamis, inda ya tabbatarwa da al’ummar kauyukan cewa gwamnati ta girka sojojinta domin su yaki ‘yan Boko Haram da zasu yi kokarin shiga cikin kasar. Yace an girka sojoji masu yawan da zasu iya takalar kowace irin barazana daga ‘yan Boko Haram.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG