Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 11 a Jihar Filato


Wasu jami'an tsaron Najeriya a lokacin da suke hanyarsu ta ai dauki
Wasu jami'an tsaron Najeriya a lokacin da suke hanyarsu ta ai dauki

A daren jiya lahadi ne wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kashe mutane sama da 10 a kudancin birnin Jos da ke jihar Filato.

Rundunar 'yan sandan jihar Filato da ke arewa maso tsakiyar Najeriya, ta tabbatar mutuwar mutum 11 a karamar hukumar Jos ta Kudu bayan wani hari da wasu 'yan bindiga suka kai a yankin.

Harin ya auku ne da misalin karfe 8:30 na dare agogon Najeriya.

Bayanai sun yi nunu da cewa maharan sun far ma unguwannin Latya da Lakwandet a cikin wata mota kirar Hilux inda suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi har suka halaka mutum 11.

Baya ga haka, wasu mutum 12 na jinya a asibiti kamar yadda wakiliyar Sashen Hausa na Muryar Amurka, Zainab Babaji ta tabbatar.

Babu dai wasu bayanai da ke nuni da cewa an samu tashin hankali a cikin garin Jos, amma matasan yankin da aka kai harin, sun yi zanga zangar nuna rashin jin dadinsu akan abin da ya faru.

Gwamnatin jihar ta Filato ta yi Allah wadai da aukuwar wannan hari, ta kuma kara yawan jami’an tsaro a yankin.

Hukumomin jihar sun kuma ce za a gudanar da bincike kan lamarin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

Facebook Forum

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG