Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan bindiga Sun Kashe Uku Daga Cikin Daliban Jami’ar Greenfield Da Suka Sace A Kaduna


Dalibai Na Rubuta Jarabawar shiga jami'a ta JAMB A Najeriya

An tsinci gawarwakin daliban uku ne a yankin Kwanar Bature a ranar Juma’a, wanda ba shi da nisa da jami’ar a cewar hukumomin jihar Kaduna.

Rahotanni daga jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya na cewa uku daga cikin daliban jami’ar Greenfield da masu garkuwa da mutane suka sace sun mutu.

A ranar Laraba ‘yan bindiga suka abka cikin jami’ar wacce ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, suka sace dalibai da dama.

Hukumomin jihar Kaduna sun tabbatar da ukuwar wannan lamari inda suka bayyan cewa an ga gawarwakin dalibai uku ne a yankin Kwanar Bature a ranar Juma’a, wanda ba shi da nisa da jami’ar.

Jami’ar Greenfield na karamar hukumar Chikun.

Bincike ya nuna cewa shekara uku da suka gabata aka bude jami’ar ta Greenfield.

Shaidu sun ce maharan sun yi ta harbi a sama kafin daga bisani su kwashe daliban su kutsa da su cikin daji a ranar da suka kai harin.

Wannan hari na zuwa ne sama da wata guda bayan da ‘yan bindiga suka sace daliban makarantar horar da ilimin albarkatun daji da ke Afaka a jihar ta Kaduna.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG