Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Sace 'Yan Mata 15 A Jamhuriyar Nijar


Taron manema labarai kan harin Diffa
Taron manema labarai kan harin Diffa

yanzu haka wasu yan bindiga sunyi awon gaba da wawsu 'yan mata goma sha biyar a cikin garin Tamur dake Jihar Diffa, lamarin da ya tada wa mutane hankali sosai. 'yan majalisun yankin sun yi kira da gwamnati ta tashi tsaye sosai akan harkokin tsaro.

A yau da safen nan ne aka samu labarin cewa wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne, jiya da daddare, sun sace wasu 'yan mata goma sha biyar a cikin garin Tumur da ke yankin Diffa.

Shekaran jiya da daddare an kashe mutane takwas a garin na Tumur, sannan akwai wani gari da ke makwabtaka da shi wato Bage da ke kusa da garin Tumur din shi ma, an ce sun yi awon gaba da 'yan mata uku.

Lamarin da ya yi matukar tada hankulan jama’ar yankin. 'Yan majalisun da su ke wakiltar yankin Diffa sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa ta hannun kakakinsu, wato Lamido Mumuni Haruna, inda su ka yi kira ga gwamnatin Jamhuriyar Nijar da ta dauki mataki akan matsalar tsaro da ake fama da ita a yankin nasu.

Ga cikakken rahoton daga wakilin mu Sule Mumuni Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG