Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gina Wani Kauyen Mata Zalla a Syria


An gina wani kauye musamman domin mata a yankin Rojave na kasar Syria. Kauyen da ake kira Jinwar, wanda a harshen Kurdawa yake nufin wurin mata, yana da rukunin gidaje da aka gina iri daya guda talatin.

Yanzu haka iyalai biyar suke kauyen, ana kuma kyatata zaton wadansu da dama zasu koma kauyen da zama. Abin da ya banbanta kauyen da sauran kauyuka shine, mata ne zalla da kananan yara ke zaune a wurin.

Abin da ake tunani shine a kafa kauye inda mata zasu zauna cikin walwala tare. Inda mata zasu iya kafa jarinsu, su yi rayuwarsu ba tare da dogara ga kowa ba.

Nojeen, wata ‘yar kasar Jamus mai aikin sa kai da ta taimaka wajen gina gidajen tace wadansu matan an kashe mazansu lokacin suna yaki da kungiyar IS, ta kuma bayyana burin ganin kauyen ya ba matan da iyalansu wani sabon babin rayuwa.

Badria Darwish tana daya daga cikin matan dake zaune a kauyen bayanda aka kashe mijinta a yaki.

Ta ce "nazo nan ne domin ba zan iya daukar nauyin ‘yayana ba. Da farko ina dari darin zuwa nan, amma na kasa kula da ‘yayana. Na zo in zauna nan tare da ‘ya’yana domin rayuwa tayi mana matukar wuya".

Wadanda suka kirkiro shirin kafa kauyen matan, sunce idan ya yi nasara, za a kara gina wadansu kauyukan a Jinwar dake arewacin kasar Syria.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG