Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Bindiga Sun Sake Afkawa Tegina; Sun Sace Ma’aikatan Wata Masana’anta


'Yan Bindiga
'Yan Bindiga

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi garkuwa da akalla mutane biyar a wani kamfanin ruwan leda a garin Tegina da ke karamar hukumar Rafi na jihar Naija.

Majiyoyi sun yi nuni da cewa a karshen makon nan ne ‘yan bindigar suka mamaye garin na Tegina, inda suka yi awon gaba da ma’aikatan wata masana’anta su biyar.

Rahotanni dai sun yi nuni da cewa ‘yan bindigar dauke da bindigogi kirar AK47 da suka kai harin sun kai kimanin 10.

Wata majiya ta ce yan bindigar sun mamaye garin ne da misalin karfe 9 na dare inda suka je wani dakin ajiyar ruwan sayarwa na leda a kusa da makarantar sakandiren ’yan mata ta gwamnati.

Mutanen da ke yankin sun ce an afka mu su a ba zata ba saboda yan bindigar sun shigo mu su da kafa, kawai mazaunan garin sun fara jin karar harbe-harbe kuma suka gudu domin tsira da rayukansu.

‘Yan bindigar sun shiga kamfanin ruwan leda inda suka kwashe mutane biyar, kamar yadda wata majiya ta sahidawa jaridar Daily Trust.

Idan ana iya tunawa ‘yan bindiga sun sace daliban makarantar Islamiyya da ke Tegina a farkon shekarar nan.

Duk kokarin ji ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta wayar salula ya ci tura.

XS
SM
MD
LG