Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

’Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Kimanin Dalibai 15 A Jihar Zamfara


Gunmen
Gunmen

Majiyoyi daga jihar Zamfara sun bayyana cewa jumlar wadanda suka rasa ransu a harin a halin yanzu ya kai hudu a yayin da mutane 19 suke hannun 'yan bindigar.

Wasu ‘yan Bindiga sun kai wani sabon hari a kwalejin horar da dabarun aikin gona da ke karamar hukumar Bakura a jihar Zamfara inda suka yi awon gaba da dalibai akalla 15, da ma’aikacin makarantar daya da matarsa da kuma ‘ya’yansu biyu.

Mazauna yankin sun bayyana cewa harin da ya auku ne a daren ranar Lahadi wayewar garin Litinin.

Majiyoyi sun ce 'yan bindigar sun halaka masu aikin gadi 3 da kuma jami’in dan sanda daya a harin.

Rahotanni na bayyana cewa jumlar wadanda suka rasa ransu a harin a halin yanzu ya kai mutum hudu, a yayin da kuma akalla mutane 19 su ke hannun 'yan bindigar.

Wani shaidun gani da ido da ya bukaci a sakaya sunansa a bisa dalilai na tsaro, ya tabbatar da afkuwar lamarin ga wakilin Muryar Amurka a jihar ta Zamfara.

To sai dai har kawo lokacin wallafa wannan labari, babu wani karin bayani daga rundunar 'yan sanda ko hukumomin gwamnatin jihar ta zamfara.

‘Yan bindiga dadi sun dade suna addabar jihohin arewa maso yamma ciki har da Zamfara, inda manazarta ke ganin lamarin ya fi kamari.

Har zuwa lokacin hada wannan labari duk kokarin tabbatar da afkuwar lamarin daga hukumar yan sanda ya ci tura.

XS
SM
MD
LG