Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Yi Wa Sojoji Kwantan Bauna A Kan Iyakar Abuja


Yan bindiga
Yan bindiga

Wasu Yan bindiga sun aukawa jami'an tsaron sojiji dake aiki a shingen Bincike na jami,an tsaro dake kusa da Dutsin Zuba ta karamar Hukumar suleja kan Babbar Hanyar Abuja a jihar Nejan Nigeria,

Bayanai dai suna cewa tun Misalin karfe bakwai na yammacin Alhamus din nan akayi misayar Harbe Harbe a wurin,

A hirar shi da Muryar Amurka, wani Direban Mota da lamarin ya faru a gaban idanunsa kuma ya nemi a sakaya subansa bisa dalilan tsaro, wanda kuma ya samu rauni a kafa, yace lamarin ya jefa su cikin tashin hanakali.
Bisa ga bayaninsa, ya ga gawarwakin mutane biyu da aka kashe sai dai ba zai iya sanin ko sojoji ne ko kuma maharan. Ya ce bisa ga dukan alamu 'yan bindigar sun isa wurin ne cikin motoci ba babur kamar yadda aka saba gani ba. Ya kuma bayyana cewa jami'an tsaro sun isa wurin kan lokaci.
Duk kokarin jin ta bakin Rundunar 'Yan sandan jihar Neja dama Gwamnatin jihar Nejan a lokacin hada rahoton ya cimma tura.
Saurari rahoton cikin sauti:
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:08 0:00
XS
SM
MD
LG