Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Boko Haram ne sun kashe kanin Shehun Borno


Market in Maiduguri, Nigeria (file photo)

Wasu wadanda ake zaton yan Boko haramun ne sun kashe kanin Shehun Borno. A gidansa aka kashe shi ranar litinin da dare

Yan Boko Haramun Ne Sun Kashe Kanin Shehun Borno
Litinin Da Dare, Yan Boko Haramun Ne Suka Kashe Kanin Shehun Borno, Abbas Anas Umar, A Gidansa A Maiduguri. Ga Rahoton Da Wakilin Sashen Hausa Haruna Dauda Biyu Ya Aiko Akan Wannan Kisa.

Yan sandan Nigeria sunyi imanin cewa wakilan kungiyar boko haramun ne keda alhakin kashe kanin Shehun Borno. Hukumomi sunce ranar litinin da dare aka kashe Abbas Anas Umar a gidansa a birnin Maiduguri. Ita dai wannan kungiyar ta yan boko Haramun ne, tun ba yau take razana jama'a, musamma a Maiduguri da Bauchi. Jami'ai sun baiyana cewa a yan watanin da suka shige, yan boko haramun ne sun yi ta aunawa, da karkashe yan sanda da yan siyasa da kuma Malamai a jihar Boirno. A shekara ta dubu biyu da tara kungiyar ta yiwa gwamnati bore da har aka yi mako guda ana dauki ba dadi tsakanin yan kungiyar da jami'an tsaro, data zama sanadin da aka kashe kimamin mutane dari

XS
SM
MD
LG