Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Sun Boye Bama-bamai a Dajin Song


Rundunar 'yansandan jihar Adamawa ta bankado wasu bamabamai da aka boye cikin dajin Song

Garin Song nada tazarar kilomita tamanin da Yola fadar gwamnatin jihar Adamawa.

Makon da ya wuce sojoji sun cafke wasu 'yan kunar bakin wake shida a garin na Yola cikinsu har da wani da yayi shigar mata. Ya nunawa manema labarai bamabaman da aka nada masa a jikinsa.

Ta bakin kwamishanan 'yansandan jihar 'yan kunar bakin waken sun shirya kai hare-hare ne wurare daban daban ciki har da babbar gadar da ta hada fadar gwamnati da arewacin jihar.

'Yansandan sun samu sun gano bamabaman ne biyo bayan tsegunta masu da aka yi inda suka samesu a binne. 'Yansandan kwance bamabamai suka je suka tonosu. Bamabaman goma sha tara aka gano wadanda an riga an danasu suna jiran su tashi ne kawai.

Kowane daya daga cikin bamabaman ka iya tarwatsa gada ko kuma ginin bene mai hawa goma. Da Allah bai kare ba babu wanda ya san irin mutuwar da za'a yi. Don haka aka kira jama'a su sa ido ga duk abun da basu amince dashi ba su kuma kai rahoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00


Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG