Accessibility links

'Yan Boko Haram Sun Fada Hannun 'Yan Bangan Kato Da Gora


'Yan bangan Fararen Hulan JTF suna anfani ne da kulake da sanduna da makaman da aka sarafa cikin gida suna sintiri a kan titunan Maiduguri, Najerya.

Wasu da ake zaton 'yan kungiya Boko Haram ne sun fada hannun 'Yan Bangan da Gora ko Civilian JTF a jihar Adamawa

A jihar Adamawa 'yan kungiyar sa kai ko 'yan banga da gora da aka fi sani da suna Civilian JTF dake taimakawa sojoji sun cafke wasu da ake zaton 'yan Boko Haram ne.

'Yan bangan sun cafke mutane dama a garin Michika a arewacin jihar Adamawa. Su 'yan bangan idan sun yi kamu sai su mikasa ga sojoji. Su dai 'yan bangan kasada suke yi domin basu da makamai illa gora da kulake shi yasa 'yan Boko Haram ke kai masu hari suna kashesu.

Wani dake zaune a garin Michika ya tabbatar da kamun mutane da 'yan banagan suka yi. Su 'yan banagan da goran daga Maiduguri ta jihar Borno suka je Michika. Ta bakin mazaunin garin 'yan bangan sun biyo 'yan Boko Haram da suka gudu daga jihar Borno suka nemi mafaka a garin na Michika. Da farko mutane 18 suka kama. Da suka bincikesu suna sasu su rantse da Kur'ani sai suka wasu. Wani ma da suka tabbatar dan Boko Haram ne sun yanke kunnensa suka bashi ya hadiye dole. Shida cikin 'yan Boko Haram din tuni aka wuce dasu Maiduguri kana guda 5 rundunar soja ta tafi da su. Wannan lamari ya faru ne kwana biyu da wasu 'yan bindiga suka kai hari a ofishin 'yansanda a garin Gombi cikin jihar Adamawa inda suka kashe 'yansanda suka kone ofishinsu da ma mota. Wannan aika-aikar ya sa aka baza 'yansan cikin garin da kewaye domin farautar 'yan bindigar.

Ana zaton 'yan kungiyar Boko Haram da dama suka sulalo daga Borno zuwa cikin jihar Adamawa sabili da fatartakar da sojoji suka yi masu bisa ga umurnin shugaban kasar Najeriya.

Ga karin bayani.
XS
SM
MD
LG