Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Boko Haram Sun Fatattaki 'Yan Sanda


Abubakar Shekau

Mayakan Boko Haram cike da mota da kuma babura biyu suka farma garin Sagieme a jihar arewa mai nisa a kasar Kamaru.

Mayakan Boko Haram sun kai wani sabon hari wanda ya halaka jandarmomi 2 a garin Sagieme dake karamar hukumar potokol a jihar arewa mai nisa inda suka kwashe awowi kusan biyu suna batakashi.

A garin Sagieme gungun maharani na Boko Haram, sun bude wuta a wani ofishin ‘Jandarmomi Sagieme, inda akayi dauki musayan wuta a tsakaninsu, wanda yayi sanadiyar mutuwar jandarmomi biyu.

Rahotani na nuni da cewa maharani Boko Haram, sun shiga garin ne da misalign bakwai da rabi ne a cikin wata mota da kuma Babura biyu inda daga bisani da jandarmomin suka ranta ana kare.

Maharan na Boko Haram dai na shiga kasar ta Kamaru ne ta kan iyakar kasar da tarayyar Najeriya. Muryar Amurka ta nemi jin ta bakin gwamnan jihar arewa mai nisa Mijinyawa mai nisa amma abin ya ci tura.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:03 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG