Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Boko Haram Sun Kai Hari A Jihohin Borno Da Yobe


Rahotanni sun bayyana cewa wasu gungun ‘yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne sun kai wasu hare-hare a karamar hukumar Damboa a jihar Borno da kuma garin Dapchi dake jihar Yobe.

Wasu mazauna garin Dapchi sun bada tabbacin cewa, wasu ‘yan bindiga sun yi ta harbe-harbe bayan haka sun kona wasu gidaje da motacin jam’ian tsaro amma daga bisani jami’an tsaron sun fatattaki ‘yan bindigar. Ko da yake, ya zuwa yanzu dai jami'an tsaro basu ce komai akan aukuwar lamarin ba.

Haka zalika a jiya Laraba wasu ‘yan bindiga sun kai hari a garin Damboa dake jihar Borno wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama ciki har da jami’an tsaro, wasu da yawa kuma sun samu raunuka.

Gwamnatin jihar Borno ta fitar da wata sanarwa ta hannun mai magana da yawun gwamnan jihar Alhaji Isa Umar Gusau, sanarwar ta bada tabbacin cewa jami’an tsaro sun samu nasara akan maharan sun kuma samu damar kwato motocin yaki guda 19, tare da kashe 'yan bindiga da dama.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:58 0:00

Facebook Forum

An Ga Watan Azumi A Najeriya - Sultan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammada Sa'ad Abubakar Ya Ba Da Sanrwar Ganin Watan Ramadan
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG