Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Boko Haram sun Mamaye Gidan Mukaddashin Gwamnan Jihar Adamawa

Mukaddashin gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri.

‘Yan kungiyar Boko Haram, a yanzu haka sun mamaye gidajen, wasu fitattun mutane a yankin Gulak da Madagli, ciki har da gidan mukaddashin gwamnan jihar, Ahmadu Umaru Fintiri, da kuma na Hakimin Duhu.

‘Yan kungiyar Boko Haram, a yanzu haka sun mamaye gidajen, wasu fitattun mutane a yankin Gulak da Madagli, ciki har da gidan mukaddashin gwamnan jihar, Ahmadu Umaru Fintiri, da kuma na Hakimin Duhu.

Bayanai sun ce mayakan Boko Haram, har yanzu na ci gaba da watayawa a wasu yankuna na Michika, duk kuwa da fafatawar da aka ce suna yin da Sojoji.

Wani da wakilin muryar Amurka ya zanta shi yace ‘yan Boko Haram din inda suka kama matasa suna tilasa masu shiga kungiyar tasu.

A yanzu kuma akwai wasu kauyawan dake tare hanya, suna farwa masu neman tserewa daga gari Michika.

Dakarun Najeriya,suna can suna fafatawa domin kwato wasu daga cikin garuruwan da ‘yan kungiyar ta Boko Haram, suka yin nasaran kwacewa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG