Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Boko Haram Sun Soma Sa Guba cikin Rijiyoyi da Tafkuna a Jihar Borno


Gwamnan jihar Borno Ibrahim Kashim Shettima

'Yan kungiyar Boko Haram da yanzu basu da kayan yaki kamar da sun fito da wani salo na sa guba a rijiyoyi da tafkuna inda mutane ke samun ruwan sha a wani yankin jihar Borno.

Kanar Tukur Gusau jami'in watsa labarai na rundunar sojojin Najeriya dake yaki da Boko Haram mai lakani Lafiya Dole a arewa maso gabashin Najeriya shi ya tabbatar da batun sa guban cikin ruwan sha.

Yace sakamakon labarin sa guba din ne ya sa babban kwamandansu dake gudanar da yakin Janar Abubakar ya umurci cewa a wayarwa jama'a kai saboda kada su fada tarkon 'yan ta'adan.

Yace sun samu labarin cewa suna zuba guba cikin rijiyoyi da kuma tafkuna a wuraren da sojoji suka fatattakesu. Sun yi kokarin gurbata ruwan sha na jama'a domin su hallakasu.

Kodayake kawo yanzu babu labarin wani mutum ya mutu sanadiyar shan ruwa mai guba amma babbobi da yawa sun mutu a bangaren da ake kira Kangalam.

Masana cikin sojojin suka tabbatar cewa ko shakka babu an sa guba cikin ruwan da dabbobi suka sha suka mutu.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG