Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sama Da ‘Yan Boko Haram 200 Ne Suka Mika Makamansu Ga Operation Lafiya Dole


Nigeria Boko Haram

Kwamandan sojojin Operation Lafiya Dole, na shiyar Borno da Adamawa da Yobe da Bauchi da Gwambe, Janar Yusha’u Muhamud Abubakar yace an sami nasarori dayawa game da yaki da suke da ‘yan bindiga masu tayar da kayar baya wato Boko Haram.

Janar Yusha’u yace, da taimakon Allah da kuma kayan aiki da suke samu shine ya taimaka ga samin nasarori a yakin da ake da Boko Haram, sojoji yanzu suna da kwazo sosai kuma sun yarda da cewa wannan yakin nasu ne kuma dole ne suyi duk abinda yakamata don ganin sun kawo karshen ‘yan bindiga.

A jiya ne da missalin karfe biyar na yamma sojojin Najeriya suka kama garin Banki, wadan garine da yake da tattalin arzikin kasa kwarai da gaske kuma ya dade a hannun ‘yan bindigar, a safiyar yau Juma’a an samu ‘yan kungiyar Boko Haram fiye da ‘dari biyu sun mika makamansu. Kamar yadda Janar Yusha’u ya bayyana sojoji na kwashe duk ‘yan bindigar da suka mika kansu zuwa wajen gari alokacin yaki, domin wasunsu sun shiga kungiyar ne a dalilin kame garin su da akayi kuma aka tilasta musu.

A baya sojoji na shan wahala ne a dalilin boma bomai da suke danawa da boyewa a kan hanyoyi, amma yanzu sojoji na amfani da wasu dabaru domin ganin an cimma nasara. Yanzu haka dai sojin na shiga suna duba cikin gari da bin daki daki don neman duk abinda zasu samu wanda suka hada da makamai da motoci.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:41 0:00
Shiga Kai Tsaye

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG