Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Boko Haram sun kashe akalla mutane 11 akan iyakar Nigeria da kasar Kamaru


Wasu mutane ke kallon irin barnar da 'yan Boko Haram ke yi
Wasu mutane ke kallon irin barnar da 'yan Boko Haram ke yi

Shedun gani da ido a arewacin kasar Kamaru sunce akalla mutane goma sha daya ne suka mutu a sakamakon harin da yan kungiyar Boko Haram suka kai kan wata bas a kusa da kan iyakar kasar da Nigeria.

Shedun gani da ido a arewacin kasar Kamaru sunce akalla mutane goma sha daya ne suka mutu a sakamakon harin da yan kungiyar Boko Haram suka kai kan wata bas a kusa da kan iyakar kasar da Nigeria.
Rahotanin da aka samu jiya Asabar, sunce a ranar Alhamis da dare aka kai harin a yankin Waza, inda yan yakin sa kai suka bude wuta akan bas din dake cike da fasinjoji.
Hukumomi gwamnati basu ce momai ba akan harin ba, to amma wani jami'in soja a yanki ya fadawa kamfanin dilanci labarun Reuters cewa tana yiwuwa an kashe mutanen da yawansu ya kai ashirin da biyar, kuma an kai mutane goma da suka ji rauni asibiti kusa da Marwa baban birnin yankin.
Samun bayanai akan irin wadannan hare hare galibi su kan dauki lokaci domin an lalata kafofin sadarwa a yankin. Kamfanin dilancin labarun Reuters ya bada rahoton cewa matafiya daga yankin da suka isa birnin Marwa ne suka tabbatar da cewa an kai harin.
Daga can Nigeria makwapciyar Kamaru kuma,shedun ganin da ido a arewa maso gabashin kasar, sunce a ranar Larabar data shige, yan yakin sa kan kungiyar Boko Haram su sace kimamin matasa da yara arba'in daga kauyen Malari na jihar Borno dake cikin lungu.
Rashin kafofin sadarwa a yankin suna dagula bada bayana irin wadannan abubuwa da suke faruwa.
Shedu gani da ido da suka isa Maiduguri baban birnin jihar Borno sunce yan yakin sa kai sun kutsa kauyen suka sace yara maza da matasa, baban cikinsu bai wuce shekaru ashirin da uku da haihuwa ba. Shedun sunce sun arce daga kauyen bayan an kai harin.
An dora wa kungiyar Boko Haram alhakin kashe dubban mutane cikin shekaru biyar data yi tana yiwa Nigeria tawaye.

XS
SM
MD
LG