Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan China Sun Mamaye Kasuwar Kwari Da Ke Kano - 'Yan kasuwa


Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II
Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II

Tare da hadin kan wasu munafukan ‘yan kasuwar Kwari dake Kano,’yan China sun mamaye kasuwarsun bar kanawa ‘yan kasuwar da kuwa

‘Yan kasuwar dake hada hadarsu a kasuwar Kwari ta Kano sun koka da yadda ‘yan China suka mamaye kasuwar.

Aliyu Bala wani dan kasuwa mai sayar da atanfa yace yanzu kasuwar Kwari kamar tasu ce domin sun mamaye kusan kashi 70 zuwa 80 na kasuwar. Yace su ne suke juyata. Su ne suke rabawa mutane kaya. Suna shiga kasuwar suna ganin duk abubuwan dake gudana.

A cewar Kabiru Musa mutum zai sayo kaya wajen hannun ‘yan China walau ka ci riba ko ka fadi. Ya kira mahukuntan kasar da su sa baki musamman sarkin Kano wanda masanin tattalin arziki ne.

To sai kwamishanan ciniki da masana’antu na jihar Kano Alhaji Ahmed Rabiu y ace suna daukan matakai domin shawo kan lamarin. Sai dai y ace akwai kalubale. Yace ‘yan Kanon su ne suka yin munafunci a lamarin. Wasunsu na hada baki da ‘yan China su bude shago kamar nasu ne amma mallakar dan China ne. Shi dan Kanon zai zauna kamar shagon nashi ne amma dan China na ciki zaune yana bin abubuwa.

Kwamishanan ya ce a suna bin sawu kuma duk wanda suka tabbatar ya keta hadin kasar suna kaiwa hukumomin tarayya domin a yi hukumci.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG